Yadda agwaluma ke taimakawa wajen magance zazzabin cizon sauro

Yadda agwaluma ke taimakawa wajen magance zazzabin cizon sauro

Wani sabon binciken ya bayyana yadda akan iya amfani da ganye da kuma sassake na itacen agwaluma wajen magance cuta ta zazzabin cizon sauro da a wani sa'in ba ta ko jin magani.

Wannan sabon binciken kimiyyar ya bayyana yiwuwar yadda za a yi samar da sunadaran antimicrobes da zasu yakar kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro wanda a turance a ke ce musu VRSA (vancomycin-resistant Staphylococcus aureus), inda a zamanin nan suke nuna ko oho ga magani.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan sabon binciken da aka wallafa a mujallai na BMC Complementary and Alternative Medicine da kuma Asian Journal of Biomedical and Pharmac*utical Sciences ta nahiyyar Asia, ka iya zamtowa sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin cizon sauro.

Agwaluma
Agwaluma

Manazarta bincike wadanda 'yan kasar Najeriya sun jarraba maganin akan beraye dake dauke da kwayoyin cutar, inda suka tabbatar da ingancin binciken nasu.

KARANTA KUMA: Sai an kai ruwa rana akan kasafin kudi na 2018 - Sanata Adeola

A yayin gudanar da binciken, masanan sun gano cewa ana iya amfani da saiwa da kuma ganyen itacen agwaluma wajen magance cutar ta zazzabin cizon sauro.

Baya ga garkuwa da cutar zazzabi cizon sauro, itacen agwalama ya kunshi sunadarai da suka hadar da; flavonoids, steroids, glycosides da kuma saponins dake taimakawa wajen kawar da cututtukan gudawa, tsayawar jini dake kwarara daga sabon rauni, cututtukan fata, ciki, baki da kuma matanci na 'ya mace.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng