Ciwon hauka ke damun Amaechi - Inji Wike

Ciwon hauka ke damun Amaechi - Inji Wike

Gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, yayi ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar kuma ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi yana tattare da cuta ta zaucewar hankali.

Wike ya bayyana cewa tabuwar hankalin da Amaechi ke fama da ita tana da nasaba ne da nakasun ci gaba da kasar nan ta Najeriya ke fuskanta.

A sakamakon hare-haren da suka afku wanda yayi sandiyar rayukan mutane da dama a jihar Ribas, ya sanya Amaechi a ranar Talatar da gabata yayi kira ga Wike akan yayi murabus daga shugabancin jihar domin rashin cancantar sa.

A yayin caccaka ta mayar da martani, gwamna Wike yace ya kamata shugaba Buhari yayi murabus a sakamakon rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta duba da yadda zaben ministocin sa ya kasance.

Ciwon hauka ke damun Amaechi - Inji Wike
Ciwon hauka ke damun Amaechi - Inji Wike

Legit.ng ta ruwaito da sanadin shafin mujallar Al'ummata inda a ranar Larabar da ta gabata, gwamnan yayi wannan caccaka a birnin Fatakwal a yayin da kungiyar Silverbird ta mika masa kyauta a matsayinsa na gwarzon ta a shekarar 2017.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Cututtuka goma da gwanda ke nesanta su da lafiyar dan Adam

Ya bayyana kamar haka, “tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Rotimi Amaechi, yana da tabuwan hankali. Shi ya sa ba zai taba gane matsalar rashin isashen tsaro da kasar ke fama da shi ba.

Yake cewa, "a sakamakon nakasun hankali da Amaechi ke fama da shi ya sanya har yanzu ya gaza gano cewar babu isashen tsaro a Najeriye, kuma yana mai bashi shawarar gabatar da kan sa a gaban likitoci domin su nazarci lafiyarsa."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: