Atiku ba zai samu tikitin takara a PDP ba, inji Omale
- Shugaban wata coci a Abuja, Emmanuel Omale ya yi ikirarin cewa ya gano Atiku ba zai samu tikitin takara a PDP ba
- Ya kuma ce jam'iyyar PDP za ta sha kaye a zaben gwamna da za'a gudanar a jihar Ekiti
- Malamin addinin kiristan ya kuma ce gwamnonin PDP za su yi yunkurin korar Atiku daga jam'iyyar
Shugaban wata coci mai suna 'Divine Hand of God Prophetic Ministeries International' da ke Abuja, Manzo Emmanuel Omale ya gano cewa tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ba zai samu tikitin takatar shugabancin kasa a jami'iyyar PDP ba.
Ya kuma ce jam'iyyar ta PDP za ta yi rashin nasara a zaben gwamnoni mai zuwa a jihar Ekiti, har ila yau, daya daga cikin gwamnonin PDP zai sauya sheka zuwa jami'iyyar APC.
KU KARANTA: PDP ta mutu a Jihar Legas, an kuma binne ta - Jam'iyyar APC
A sanarwar da ya fitar jiya a garin Abuja, Malamin addinin kiristan ya ce ya gano cewa gwamnonin jam'iyyar PDP za su yima Atiku zagon kasa domin ya fice daga jam'iyyar amma ya kuma jadada cewa Atikun ne kadai zai iya fidda jam'iyyar daga kunya.
"Na gano kallubale sosai game da takarar shugaba Muhammadu Buhari domin ana bukatar addu'o'i sosai domin samun karbuwar sa" inji shi
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya suyi addu'o'i ga uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da wasu 'yan Majalisar Tarayyah.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng