Gwamnatin Ganduje za ta saki Naira Miliyan 300 ga ‘Daliban Jihar Kano
- Gwamnatin Kano za ta saki makudan kudi don tallafawa ‘Daliban ta
- Za a ba ‘Daliban Kano kusan 25000 da ke karatu a Najeriya gudumuwa
- Gwamnati mai-ci ta fi kowace damuwa da karatun yara Inji Hukumar
Mun samu labari mai dadi cewa Gwamnatin Jihar Kano za tayi wa ‘Daliban ta ruwan sama. Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje dai zai biya ‘Daliban cikin gida tallafin karatu a cikin ‘Yan kwanakin nan.
Gwamnatin Jihar Kano za ta ba asalin ‘Yan Jihar ta da ke karatu a cikin Najeriya kudin gudumuwa bayan ware har Naira Miliyan 300 ga ‘Daliban Jihar 24,901 da ke Jami’o’i da sauran Makarantu na gaba da Sakandare a fadin Najeriya.
KU KARANTA: Kwankwaso na da ikon zuwa Kano idan ya na so - Ganduje
Farfesa Fatima Umar wanda ita ce Shugabar Hukumar tallafawa karatun gaba da sakandare na Jihar ta bayyanawa manema labarai wannan. Farfesa Umar tace kudin ya taru a sanadiyyar biyan ‘Daliban kudin na su da ba ayi ba a da.
Umar ta zargi Gwamnatin da ta shude da kin biyan wadannan kudi daga 2011 zuwa 2015. Farfesar tace Gwamnatin Ganduje ta biya kusan Naira Miliyan 360 domin cigaban karatun Jama’ar ta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng