Dubi dukiyar da aka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas

Dubi dukiyar da aka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas

- Hukumar 'yan-sanda ta kama Alaka​, shugaban kungiyar matsafa ta Badoo, a Legas

- Kazalika hukumar ta kwace wasu kadarori da matsafin ya mallaka

- A jiya hukumar 'yan-sanda ta cafke Alaka

Hukumar 'yan-sanda a jihar Legas ta kwace wasu kadarori da suka hada da gidan man fetir, Otal, da wurin yin taro mallakar Alhaji Alaka Abayomi Kamal, wanda hukama ta ce shine shugaban wata kungiyar tsafi da ake kira Badoo.

Dubi dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas
Dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas

A ranar 22 ga watan Disamba ne hukumar 'yan-sanda ya bayyana neman Alaka ruwa a jallo bisa nasabar da yake da ita da wasu kashe-kashe masu alaka da tsafi a jihar Legas.

Dubi dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas
Gidan Mai mallakin shugaban kungiyar matsafa a Legas

A jiya kwamishinan 'yan-sanda a jihar Legas, Imohimi Edgal, ya sanar da nasarar jami'ansa na cafke Alaka tare da gabatar da shi a gaban manema labarai.

Dubi dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas
Manyan gidaje mallakin shugaban kungiyar matsafa a Legas

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kori jami'anta tara, ta ragewa wasu 25 mukami

Dubi dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas
Dukiyar da 'yan-sanda suka kwato daga hannun shugaban kungiyar matsafa a Legas

Alaka ya amsa laifin aikata kisa domin dalilan tsafi a sansaninsu tare da zama jagora ga jami'an ya zuwa Ijebu-Ode inda aka yi nasarar kama babban mai bayar da kayan tsafi ga 'yan kungiyar, Fatai Adebayo.

Kungiyar tsafi ta Badoo ta jima tana aikata aiyukan ta'addanci a sassan jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng