Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama makiyaya 8 kan kisan mutane 17 a jihar Benue
Rundunar yan sandan jihar Benue sunce sun kama makiyayya takwas kan kisan mutane 10 da kuma masu gadin dabbobi bakwai a kananan hukumar Guma da Logo dake jihar a ranar Litinin.
ASP Moses Yamu, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Labara a Makurdi.
Ya kara da cewa rundunar ta tura Karin jami’anta zuwa yankin dake fuskantar tashin hankalin domin dawo da zaman lafiya a tsakanin mutane.
KU KARANTA KUMA: Labaran Maku ya roki yan Boko Haram da su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya
Yamu ya bayyana cewa an daidaita al’amura a kananan hukumomin guda biyu yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng