Muhimman abubuwa takwas da suka faru wajen daidaita siyasa a 2017

Muhimman abubuwa takwas da suka faru wajen daidaita siyasa a 2017

Shekarar 2017 ta tafi ta bar baya da kura a siyasar Najeriya. Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta kawo jerin muhimman abubuwa takwas da suka wakana a shekarar da ta gabata ba tare da yin la'akari da tsarin lokuta da kuma yadda suka faru ba.

Muhimman abubuwa takwas da suka faru wajen daidaita siyasa a 2017
Muhimman abubuwa takwas da suka faru wajen daidaita siyasa a 2017

1. Hukumar zabe ta kasa INEC, ta fitar da jadawalin zaben kasa da za a gudanar a shekarar 2019

Hukumar ta kayyade ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, 2019 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya. Sai kuma ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2019, a matsayin ranar gundanar da zaben gwamnonin jihohi da 'yan majalisun su.

2. Hukumar INEC ta yiwa sabbin jam'iyyu 21 rijista

Hukumar zabe ta kasa ta yiwa sabbin jam'iyyu 21 rijista a watan sanarwa da sanadin shugabar labarai ta hukumar; Misis May Agbamuche-Mbu.

3. Shugaba Buhari ya nadin mukamai a cibiyoyin gwamnati da bai taba kamarsa ba

A wata sanarwa da sanadin sakataren gwamnati na kasa, Boss Gida Mustapha, shugaba Buhari ya nadin shugabannin cibiyoyi na ma'aikatun gwamnati 209 da kuma mambobin cibiyoyin 1,258.

4. Jam'iyyar APC ta gaza gudanar da taronta na gangami a shekarar 2017

5. Kotun kolu ta Najeriya ta sulhunta rikicin shugabancin jam'iyyar PDP

Kotun kolu karkashin jagorancin mai shari'a Walter Onnoghen ta sulhunta rikicin shugabancin jam'iyyar PDP a tsakanin Sanata Ahmed Makarfi da ALi Modu Sheriff a ranar 12 ga watan Yuli, 2017, inda kotun ta tabbatar da Makarfi a matsayin shugaban jam'iyyar.

6. Jam'iyyar PDP ta gudanar da taron gangami har kashi biyu a shekarar da ta gabata

Jam'iyyar PDP ta gudanar da gangamin ta na farko a ranar 12 ga watan Agusta, watanni biyu kenan bayan da kotun kolun ta zartar da shari'a akan rikicin shugabancin jam'iyyar.

Jam'iyyar ta sake gudanar da wani taron na gangami a ranar 9 ga watan Dasumba, inda aka gudanar da zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

7. Atiku ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa tsohuwa jam'iyyarsa ta PDP.

8. Sabuwar jam'iyyar PDP ta kunno kai

A sakamakon rashin amincewa da zaben shugabannin jam'iyyar PDP da ta gudanar a gangamin ta na ranar 9 ga watan Dasumba, inda Prince Uche Secondus yayi nasarar lashe zaben. Hakan ya fusata wasu mambobin jam'iyyar da har suka bangare wajen bude ta su sabuwar jam'iyyar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng