Hotuna: Tambuwal ya karrama sabbin 'yan sanda 'yan asalin jihar Sokoto
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya karbi bakuncin sabbin 'yan sanda 'yan asalin jihar Sokoto
- Ya yi kira da su zama wakilan jihar na kirki a duk inda suka samu kansu
- sunyi godiya ga gwamnan bisa kulawa da goyon bayan da ya nuna masu
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karrama sabbin manyan jami'an 'yan sanda da suka kammala karbar horo a makarantar 'yan sanda ta Jos, a watan Disambar shekarar 2017.
Tambuwal ya taya su murnar kammala horon cikin nasara tare da yi masu fatan alheri a cikin aikin da zasu fara a cikin satin farko na shekarar 2018.
DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kori jami'anta tara, ta ragewa wasu 25 mukami
Jami'an 'yan sandan sun yi godiya ga gwamna Tambuwal bisa tallafi da goyon baya da ya nuna masu yayin da suke makarantar karbar horo tare da bashi tabbacin zasu tsare mutunci aikinsu da na jihar Sokoto a duk inda suka samu kansu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng