Bazaku iya kayar da Buhari a 2019 ba – Tsohon kakakin PDP ga jam’iyyar adawa
- Wani tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina, Ya’u Umar Gojo-Gojo, yace jam’iyyar PDP ta saka hannu a aikin banza da ba zai samar musu nasara ba kan shugaba Buhari a 2019
- Gojo-Gojo yana da matukar yarda cewa jam’iyyar adawa baza ta iya karban mulki ba a jihar Katsina a zabe mai zuwa
- Yace gwagwarmayar da PDP ke cigaba da yi don ganin ta amshe kujerun shugabancin kasa da na gwamna ba abun sa rai bane
Ya’u Umar Gojo-Gojo, tsohon kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina kuma dan takaran sanata a Arewacin Katsina a jam’iyyar PDP a zaben 2015 da ya gabata, ya bayyana cewa jam’iyyar adawa baza ta iya kada shugaba Muhammadu Buhari a 2019 ba.
Ko da yake Buhari ai bayyana ra’ayinsa ban a sake neman takara ba, Gojo-Gojo wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yace gwagwarmayar da PDP ke cigaba da yi don ganin ta amshe kujerun shugabancin kasa da na gwamna ba abun bane mai yiwuwa.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Gojo-Gojo yayi magana ne a lokacin bude taron shawarwari na jam’iyyar APC, ya kara da cewa nasarar gwamnatin Masari, akwai sabani game da furofaganda da jam’iyyar PDP ta yada, wannan ya janwo asara ga jam’iyyar adawa a jihar.
A cewar shi, sauya shekar tsoffin shuwagabannin jam’iyyar PDP a jihar shaida ce cewa jam’iyyar adawa tana yaki mara nasara.
Mambobin taron, a cewar rahoto, tana dauke da tsohon shugaban karamar hukumar Batagarawa a karkashin gwamnatin jam’iyyar PDP, da kwamishinan ayyuka da sufuri, Tasi’u Dahiru Dandagoro, a matsayin sakatare.
Hade da tsohon kwamishina a gwamnati da ta gabata, Musa Adamu Funtua, da tsohon shugaba a jam’iyyar PDP, Tukur Iliyasu Shagumba, a matsayin mataimakin shugaban taron da ma’aji.
KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sandan Najeriya ta kama gagaruman yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane (hotuna)
Tsoffin mambobin jam’iyyar PDP wadanda suka kasance cikin taron sun hada da Kwamred Bilyaminu Rimi, Abdullahi Tandama, Yusuf Barmo, Mohammed Ilalla da Ibrahim Teacher da sauransu.
Mataimakin shugaban Jam’iyyar a yankin mazabar Funtua, Bala Abubakar Musawa, ya yabi gwamnatin Masari inda yace baza a iya kwatanta gwamnatin ba da nan a jam’iyyar PDP da ta share shekaru 16 tana mulki. Shitu yace yana da tabbacin cewa jam’iyyar APC zata daukaka jihar Katsina kamar yanda ya bukaci magoya jam’iyyan da su cigaba da nuna biyayya da jajirci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng