Dubi gangariyan motocci da kamfanin Innoson ta sayar wa Sojin Najeriya

Dubi gangariyan motocci da kamfanin Innoson ta sayar wa Sojin Najeriya

A yau Talata 12 ga watan Janairu na 2018 ne Hukumar Sojin Najeriya ta kammala yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da kamafanin sarrafa motoci na Innoson. Sanarwan ya fito ne bayan taro tsakanin shugaban kamfanin, Dacta Innocent Chukwuma da shugaban hafsoshin Sojin Najeriya Laftanant Janar Tukur Buratai.

Shugaban Sojin ya bayyana cewa Hukumar sojin sun saya motocci uku daga kamafanin a shekarar bara kuma sun gamsu da igancin motocin, hakan ne yasa Hukumar ta shiga yarjejeniyar. Bugu da kari hakan zai taimaka wajen bunkasa kamfanonin mu na gida. Hakan yasa Hukumar ta Sojin Najeriya ta sake sayan wasu motoccin guda 70 wanda ake amfani dasu wajen yakar 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya a karkashin Operation Lafiya Dole.

A jawabin sa wajen taron, Shugban kamfanin Dacta Innoson Chukwuma ya bayyana farin cikin sa bisa yadda hukumar ta sojin suka yaba da motoccin da suka saya, ya kuma mika godiyarsa gare su domin nuna kishin kasa da sukeyi. Ya kuma yi alkwarin cewa kamfanin zata bude wasu rassa a wasu yankunan Najeriya.

Labari cikin hotuna: Hukumar Soji ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da kamfanin Innoson

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164