Makiyan Iran ne suka haddasa zanga-zanga- Khamenei
- Jagoran addini a kasar Iran ya zargi makiyan kasar da haddasa zanga-zanga a kasar
- Ayatollah Ali Khamenei ya ce makiyan Iran na amfani da kudi makamai, siyasa da bayyana sirri dan haddasa fitina a jamhuriyyar Musulunci
- A makon da yagaba ta 'yan kasar Iran suka fara zanga-zangar nuna rashin goyon bayan gwamnatin Hassan Rouhani
Shugaban addini a kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya zargi makiyan kasar Iran da haddasa zanga-zangar da ta yi sanadiyar rasa rayuka a kasar.
Wannan shine karo na farko da, Ayatollah Ali Khamenei, yayi magana tun da aka fara zanga-zanga a makon da gabata wasu sassan kasar Iran
Mutanen kasar Iran na zanga-zanga ne saboda tsadar kayan abinci, rashin aikin yi da kuma yake-yaken da Iran ta ke yi a kasar Syria, Iraki, da Yaman.
Rohatanni sun nuna an kashe akalla mutane 22 tun da aka fara zanga-zanga a makon da ya gabata.
KU KARANTA : An bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mukamin sa na ministan mai
A wani sako da, Ayatollah Ali Khamenei, ya wallafa a shafin sa na tuwita, yace makiyan Iran na amfani da kudi makamai, siyasa da bayyana sirri dan haddasa fitina a kasar.
Ayatollah Ali Khamenei, yace nan gaba zai gabatar da jawabin ga mutanen kasa game da ainihin abun dake faruwa a kasar Iran.
Masharhanta sun ce shugaban addinin na hannunka mai sanda ne ga kasar Isra'ila, Amurka da kasar Saudiya wadanda yake nufin makiyan Iran.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng