Abuja: Fadar shugaban kasa ta kira taron gaggawa yadda za a kawo karshen wahalar man fetur
- Fadar shugaban kasa na ganawa da masu ruwa da saki yadda za a magance matsalar man fetur
- Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya jagoranci taron a madadin shugaba Muhammadu Buhari
- Shugaba Buhari ya jaddada cewa duk wadanda suke da hannu a lamarin man fetur za su hadu da fushin gwamnatinsa
Fadar shugaban kasa na ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur na Najeriya kan wahalar man fetur da ta ki cinyewa a kasar.
Ganawar wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya jagoranta a madadin shugaba Muhammadu Buhari.
Ana gudanar da taron ne a tsohon dakin taro na Banquet Hall da ke Aso Villa.
Mataimaki na musamman a kan harkokin yada labarai ga shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya tabbatar da ganawar da bidiyo a shafinsa ta Twitter.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya na shirin kara kudin tikitin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
A cewar Ahmad, shugaba Buhari ya gana da ministan sufuri kafin wannan ganawar.
Idan baku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa shugaba Buhari a sakon murnar sabuwar shekara ya bayyana cewa gwamnatinsa bata amince da irin wannan matsalar da al’ummar kasar ke fama da ita ba ganin yadda kamfanin NNPC ta dauki matakai don tabbatar da samun man fetur a duk fadin kasar.
Shugaban ya jaddada cewa duk wadanda suke bayan wannan lamarin za su hadu da fushin gwamnatinsa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng