Ana yi mana kisan sunkuru - Fulanin jihar Adamawa
- Wata kungiyar Fulani ta koka bisa kisan Fulani a jihar Adamawa
- Shugaban kungiyar Miyetti Allah ya ce kabilar Bachama na kashe Fulani a karamar hukumar Numan
- Sun yi zargin cewar an sace masu shanu fiye da 500
Wata kungiyar Fulani ta koka bisa kisan Fulani a sirrance a kananan hukumomin Numan, Demsa, da Lamurde, a jihar Adamawa.
Kazalika kungiyar ta ce an sacewa Fulanin shanu fiye da 500 a cikin kwanankin nan. Kungiyar ta yi kira da gwamnati da ta kawo masu agajin gaggawa domin gudun kure hakurin Fulanin da ka iya kaiwa su fara daukan fansa ko kuma su kare kansu.
Kimanin mutane 100 ne suka mutu a karshen shekarar 2017 a rikicin Fulani makiyaya da manoma a yankin da kabilar Bachama keda rinjaye a kananan hukumomin Numan, Demsa, da Lamurde.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen yankin arewa maso gabashin Najeriya, Mafindi Umaru Danburan, ya zargi 'yan kabilar Bachama da kokarin karar da kabilar Fulani.
DUBA WANNAN: Alkalin Kotun dake sauraron karar Dino Melaye ya mutu yayin addu'a a Coci
"'Yan kabilar Bachama sun dade da bayyana yankinsu a Numan a matsayin mai hatsari ga kabilar Fulani, kuma tun bayan wannan ikirari da suka yi suke kashe Fulanin a wani salo na yakin sunkuru," inji Danburan.
Danburan ya ce ana cigaba da kashe Hausa - Fulani da hanya ke bi da su ta garuruwan kabilar Bachama, musamman a hanyoyin yankunan Gyawana, da Lamurde-Tigno. Hakazalika Fulanin sun zargi 'yan kabilar Bachama da saka haramtattun shinge a hanyoyin wucewar dake yankinsu.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Adamawa, Othman Abubakar, ya tabbatar da samun rahoton saka haramtattun shinge a kan wasu hanyoyi tare da bayar da tabbacin cewar hukuma ba zata kasa a gwuiwa ba wajen zakulo masu hannu cikin aiyukan ta'addanci da kuma tabbatar da sun fuskanci fushin hukuma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng