Yanzu Yanzu: Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau ya bayyana a sabon bidiyo

Yanzu Yanzu: Shugaban kungiyar Boko Haram Shekau ya bayyana a sabon bidiyo

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana a sabon bidiyo da aka saki a yau, 2 ga watan Junairu, 2018.

A cewar rahoton, Shekau yayi ikirarin cewa Boko Haram da alhakin kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya a lokacin bukukuwan da akayi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shekau yayi magana cikin harshen Hausa a sakon bidiyon mai mintuna 31.

Ya ce: “Muna cikin koshin lafiya kuma babu abun da ya same mu.

“Sojojin Najeriya, yan sanda da wadanda ke shirya makirci akan mu bazasu iya yi mana komai ba, sannan kuma bazasu ci ko wani riba ba.

“Mun kai hare-hare a Maiduguri, Gamboru, a Damboa. Mune muka kai dukka hare-haren.”

KU KARANTA KUMA: Buhari bai da ra’ayin takarar shugabancin kasa a zaben 2019 tukuna - Ojudu

Jaridar New Telegraph ma ta ruwaito cewa bidiyon ya kuma nuna sahu daga harin da aka kai tashar sojoji a ranar Kirsimati a kauyen Molai dake Maiduguri.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel