Wayar wutar lantarki ya kashe mutum daya, da kona gidaje shida a Calabar
- A ranar jajibarin sabuwar shekara 2018, wayar wutar lanatarki ya kashe mutum daya a Calabar
- Sau uku wutan lantarki yana kashe mutane a cikin shekara daya a garin Calabar
Sau uku kenan wayar wutar lantarki yana kashe mutane a cikin shekara daya a Calabar, jihar Cross River.
A ranar Lahadi ne wayar wutar lanatarki yayi sanadiyar mutuwar mutum daya da lalata gidaje shida a Calabar.
Al’amarin ya faru ne, a ranar Lahadi da misalin karfe 7.30 na yamma wanda ya raunana mutane biyu a gida mai lamba 17 Umo Orok Lane Calabar.
A ranar, 20 ga watan Maris, 2017, mutane takwas suka rasa rayukan su ta sanadiyar fadowar wayar wutar lantarki a samar rufin gidan kallon kwallo a lokacin da mutane ke kallo wasan kwallo a jihar Edo.
KU KARANTA : Masar ta yanke wa tsohon shugaban kasa Morsi tare da mutane 19 shekaru uku a gidan kaso bisa laifin zagin hukumar shari'ar kasar
Bayan haka a watan Oktoba na shekara 2017 wayar wutar lantarki ya kara kashe mutane biyu a unguwar Adak Uko dake Calabar da kona gida daya.
Rahotanni sun nuna cewa, karfin wutar lantarki ya janyo mumunar hatsarin da ya faru a ranar Lahadi, wanda yayi sanadiyar konewar gidaje shida da kashe wani matashi dan kasuwa mai suna Joseph.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng