Kimani mutane 158 suka mutu a hadari na hanya a jihar Katsina a shekarar 2017 – Inji FRSC
- Hukumar FRSC ta ce kimani mutane 158 suka mutu a hadarin hanya a jihar Katsina a shekarar 2017
- Hukumar ta ce an samu yawan hadari na hanya 284 wadanda suka shafi motoci 466 a fadin jihar
-Babban Kwamandan FRSC ya bukaci masu motoci su daina yin amfani da gajiyayyen tayoyin mota mara kyau
Hukumar tabbatar da tsaron hanyar mota na tarayya (FRSC) ta ce kimanin mutane 158 suka rasa rayukansu a hadarin mota a fadin jihar Katsina a shekara ta 2017.
Mista Godwin Ngueku, babban kwamandan hukumar FRSC a jihar, ya bayyana hakan a wata hira da majiyar Legit.ng a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba a Katsina.
"Kimani mutane 183 ne suka halaka a hadarin mota a 2016 da kuma mutane 158 a shekara ta 2017, wannan ya nuna raguwar asarar rayuka da ake samu a hadarin mota a jihar, wanda shine daya daga cikin manufofin hukumar FRSC", in ji shi.
Ya ce an samu yawan hadari na hanya 284 wadanda suka shafi motoci 466 a fadin jihar.
KU KARANTA: Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Taraba
Ngueku ya kara da cewa mutane 1,749 suka kasance a cikin hatsarori, yayin da mutane 993 suka samu raunuka daban-daban.
Ya daganta manyan abubuwan da ke jawo hatsarorin a matsayin obalodi, gudu, ganganci ga tuki da sauransu.
Ngueku ya bukaci masu motoci su ci gaba da bin dokoki da ka'idojin zirga-zirga, da kuma dakatar da yin amfani da gajiyayyen tayoyin mota mara kyau a matsayin wani ɓangare na kiyaye haduran hanya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng