Yanzu-yanzu: Anyi wani mummunan hatsarin mota a babban titin Ibadan zuwa Legas
- Anyi wani mummunan hatsarin mota a babban titin Ibadan zuwa Legas
- Hatsarin ya jawo salwantar rayuka biyar da jikkata wasu 13
- Hatsarin ya faru da safiyar yau ne
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta sanar da afkuwar wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu mutane 13.
Shugaban hukumar FRSC reshen jihar Ogun, Mista Clement Oladele, ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa a wata ganawar su a yau. Ya ce hatsarin ya faru ne a Wazobia da misalin karfe 9:00 na safe.
DUBA WANNAN: Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji
Oladele ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wasu motoci biyu kuma ya shafi mutane 18. Biyar sun mutu yayin da 13 suka samu raunuka daban-daban.
Wata motar fasinja ce dake tafiya Legas ta kwace kuma ta yi karo da wata tirela.
"Gawar wadanda suka mutu na ajiye a dakin adana gawa na asibitin Ipara, yayin da wadanda suka samu raunuka ke karbar magani a asibitocin Sagamu da Ogere," a cewar Odele.
Odele ya bayyana cewar direban karamar motar tuni ya tsere bayan afkuwar hatsarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng