Kisan gilla: An saki rahoton yawan barnar da Boko Haram tayi
- Wannan kididdigar ta jihar Adamawa ce kawai
- Kididdigar wata kungiyar musulmi ce tayi, kuma ta bi kananan hukumomi 6 ne kacal
- Mutum 5,247 ne suka mutu a yankin a shekaru 4
Wata kididdiga da wata kungiyar musulmi tayi tace kisan gillar Boko Haram a yankunan Madagali, Michika, Maiha, Mubi North, Mubi South, Hong da Gombi kadai ya kashe akalla mutum 5,247.
Kashe-kashen, sun faru ne a jihar a shekarun 2013 zuwa 2017, kuma a cewar kungiyar, wadanda suka rasa rayukan nasu dukkansu musulmi ne.
DUBA WANNAN: Saboda an saya mai aiki waya take ta fushi
Rahoton, wanda shugaban kungiyar, Abubakar Magaji, da Secretary General, Ismaila Umaru suka sanya wa hannu, sun kuma ce mutum 5,161 ne suka sami raunuka a tsakanin.
Har yanzu dai ana fafatawa da kungiyar Boko Haram a yankin, inda suka koma yakin sunkuru da kunar bakin wake.
Su dai mayakan sun ce duk wanda bai bi irin fahimtar su ba, kafiri ne, kuma jininsa ya halatta, wanda hakan ya basu damar kashe mutane ba ji ba gani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng