Gwamnatin Iran tayi barazanar babban taku muddin zanga-zanga bata tsaya ba
- Ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a biranen Iran
- Mabiya gwamnati suma sun fito nuna soyayyarsu ga shugabanninsu
- Gwamnati tace masu adawa su koma gida ko su fuskanci hukuma
Kasar Iran ta shiga kwana na ukku ana buga zanga-zanga a manyan biranen kasar ta, wanda aka faro ranar juma'a, kuma har an fara samun asarar rayuka.
A jiya kuma masu biyayya ga gwamnati suma sun fito a babban birnin domin nuna soyayya ga shugaba Rouhani da ma Mista Khamenei, babban limamin kasar.
Sai dai gwamnati a yau tayi kira da masu adawa da zanga-zanga da su koma gida ko su fuskanci fushin hukuma, kamar yadda BBC ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Wani mai ikirarin annabta ya ce ya gano gobe
Tun a 2009 da aka yi irin wannan muzahara, wadda da yawa suka mutu, ba'a kara samun irin wannan tashin-tashina da ta kai wannan girma ba, kuma hukumomi basu so kasar ta shiga rikici kamar yadda ta faru a sauran kasashen yankin.
Masu zanga-zangar dai na kira da a kawo karshen matsin tattalin arziki, da tsauraran matakai dagwamnati ke dauka kan 'yancin 'yan kasa da sunan addini, musamman mika kudaden kasar ga mayaka a wasu kasashen, maimakon habaka arzikin cikin gida.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng