Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji

Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji

- Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya lalace a tsakiyar jeji

- Jirgin na hanyar sa ta zuwa Kano ne daga Legas

- Mafi yawan fasinjojin jirgin na tafiya Kano ne domin yin bikin sabuwar shekara da iyalansu

Wani jirgin kasan fasinjoji dake hanyar sa ta zuwa Kano daga Legas ya samu matsala a tsakiyar jeji dake nesa da babban birnin Osogbo a jihar Osun.

Mafi yawan fasinjojin dake cikin na hanyar su ta zuwa Kano domin bikin sabuwar shekara da iyalansu. Saidai a halin yanzu sun fara fitar da tsammanin cikar wannan buri na su.

Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji
Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji

Wani daga cikin fasinjojin jirgin kuma matashi mai hidimtawa kasa ya fadawa jaridar Daily Trust cewar tun bayan samun matsalar jirgin, jami'an hukumar kula da jiragen kasa dake cikin jirgin sun gaza yin abinda ya kamacesu ta fuskar nuna damuwa ko kulawa ga fasinjojin dake cikin jirgin.

DUBA WANNAN: Wani fasto ya rataye kansa a jihar Kaduna

Matashin ya kara da cewa "Wannan jirgin yana tafiya zuwa Kano ne daga Legas, amma ya samu matsala jim kadan bayan barin Osogbo. Muna tsakiyar daji tun misalin karfe 7 na safe, ga shi har yanzu babu cigaba da aka samu. Muna cikin mawuyacin hali, domin gaskiya muna shan wahala, ga shi jami'an hukumar NRC dake cikin jirgin basu da kyakykyawar mu'amala da mutane".

Hakazalika ragowar fasinjojin dake cikin jirgin sun koka da halayyar ma'aikatan jirgin ta nuna halin ko-in-kula da halin da fasinjojin suka tsinci kansu.

Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji
Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a tsakiyar daji

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: