Dan wasa Cristiano Ronaldo na neman barin Kungiyar Real Madrid

Dan wasa Cristiano Ronaldo na neman barin Kungiyar Real Madrid

- Real Madrid ta fara shirin saida babban ‘Dan wasan ta

- Ronaldo ya nuna niyyar sa na barin Real Madrid a badi

- Kulob din za ta nemi akalla Miliyan €100 kafin ta sake sa

Mun samu labari cewa Kungiyar Real Madrid tayi wa babban ‘Dan wasan ta Cristiano Ronaldo kudi bayan da ‘Dan wasan ya nuna cewa yana da niyyar tashi daga kulob din a shekara mai zuwa.

Dan wasa Cristiano Ronaldo na neman barin Kungiyar Real Madrid
Real Madrid na shirin saida babban 'Dan wasan ta

Rahoton da mu ka samu ya nuna cewa Kungiyar tana neman akalla Dala Miliyan €100 ga duk mai shirin sayen babban ‘Dan wasan na Duniya. Jaridar Daily Record ce tace ‘Dan wasan na shirin barin Santiago Bernabeau.

KU KARANTA: Ronaldo zai koma harkar fina-finai idan ya ajiye kwallo

Yanzu haka akwai kishin-kishin din cewa abubuwa sun cabe tsakanin gwarzon ‘Dan wasan na Kasar Portugal da Shugaban Kulob din Florentino Perez. Ana cewa yanzu haka ko magana ba ya hada Ronaldo da Perez.

Idan Real Madrid za ta saida ‘Dan wasan, Kungiyoyi irin su Manchester United da PSG za su fara shirin tara kudi don badi. Kwanaki ‘Dan wasan ya kara zama gwarzon Dan wasan Duniya a kulob din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng