Wani Fasto mai kiran kansa annabi ya fadi abubuwan duk wai da zasu faru a badi

Wani Fasto mai kiran kansa annabi ya fadi abubuwan duk wai da zasu faru a badi

- An saba jin Pastoci suna fadin su annabawa ne, kuma wai suna iya warkar da cutuka

- Akwai su da karbar kudaden sadaka, sai dai ana ganin su a jirage da motoci da gidaje na kasaita

- Sukan ce suna da karfin gani-har-hanji, kuma ana musu wahayin mai zai faru 'a gobe'

Wani Fasto mai kiran kansa annabi ya fadi abubuwan duk wai da zasu faru a badi
Wani Fasto mai kiran kansa annabi ya fadi abubuwan duk wai da zasu faru a badi

Wani fasto mai suna Apostle Ogochukwu Amaukwu wanda ya ce shi ma annabi ne da ake yi wa wahayi, ya saki bayanai da yace wai abubuwa ne da zasu faru a shekarar 2018.

A cewarsa dai, shugaban cocin Excellent Christian Ministry International yace ya gano me zai faru ga duniya, me zai faru ga Najeriya, kuma me zai faru da wasu mutane, musamman masu kudi da masu siyasa, sai dai da yawa daga irin wadannan zantuka basu da ma kan gado.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta kama kudade daga bankuna kan kin biyan haraji

A cewarsa dai, Atiku Abubakar ba zai kai labari a burinsa ba, sannan wai shugaba Buhari zai dawo yayi rashin lafiya, gwamnati kuma zata takurawa kirista a arewa, sannan kuma ma wai za'a yi girgizar kasa a Najeriya, hadi da sauke manyan hafsoshin soji.

Ko a baya ma wani Fasto mai suna TB Joshua, wanda yake kurarin ya gano gobe, ya sha kunya bayan da yace mace ce zata ci zabukan shugabancin Amurka na bara, amma hakan bata yiwu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng