Ki ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta shawarci Aisha Buhari

Ki ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta shawarci Aisha Buhari

- Aisha Yusufu ta shawarci matar shugaban kasa ta ceci rayuwan dan ta

- Shugaban kungiyar BBOG ta shawarci Aisha Buhari ta tabbatar da an kai Yusuf asibiti mai kyau dan samun kyakyawar kulawa

Aisha Yesufu, shugaban kungiyar masu fafutikar neman dawo da yan matar Chibok BBOG, ta bukaci matar shugaban kasa Aisha Buhari ta ceci rayuwan danta.

Ta ce matar shugaban kasa ta tabbatar da an kai dan ta da yayi hatsari akan babur a makon da yagabata asibiti mai kyau dan samun kyakyawar kulawa.

Aisha Yusufu ta bayyana haka ne a shafin ta na tuwita a rana Asabar.

Ke ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta fadawa Aisha Buhari
Ke ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta fadawa Aisha Buhari

A jawabin da Aisha Yesufu ta yi, ta ce kada a kuskura a dauki al’amarin Yusuf Buhari da wasa, saboda jin ciwo a kai ba abun wasa bane.

KU KARANTA : Aisha Buhari ta koma a asibitin da Yusuf ke jinya

Ta rubuta a shafin ta na tuwita kamar Haka @ Mrs Aisha Muhammadu Buhari wannan sako ne daga mahaifiya zuwa wajen mahaifiya. Ina fatan kina lafiya.

“Ina son ki tashi daga kan gadon da kike a kwance , ki ceci rayuwar dan ki, saboda yana bukatar ki fiye da kowa a yanzu."

“Mahaifiya kadai za ta iya kare rayunwa yayanta .Saboda haka ki tashi tsaye ki yanke hukunci mai kyau akan rayuwan danki, ki tabbatar da an kai shi asbiti mai kyau, saboda jin ciwo a kai ba abun wasa bane."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: