Iran ta mayar wa da Amurka martani

Iran ta mayar wa da Amurka martani

- Gwamantin Iran ta ce Amurka ba ta da hurumin fadawa mutanen ta yadda za su nemi hakkin su

- Amurka ta zargi gwamnatin Iran da musugunawa masu zanga-zanga akan tsadar rayuwa a kasar

Gwamnatin kasar Iran ta mayar wa kasar Amurka maratani akan zargin da take mata na musugnawa masu zanga-zanga a kasar.

A sanarwar da Iran fitar a ranar Asabar ta ce, Amurka bata da hurumin fadawa mutanen iran yadda za su nemi hakkin su a dimokradiyyance.

Iran ta mayar wa da Amurka martani
Iran ta mayar wa da Amurka martani

Shugaban maa’ikatar harkokin waje na kasar Iran, Behram Kasimi ya ce, Gwamnatin Iran tana goyon bayan duk wani hanya da za a bi wajen warware matsalolin da kasar ke fuskanta matukar bai sabawa tsarin mulkin kasar ba.

KU KARANTA : Samari a kasar Iran suna zanga-zangar kin jinin gwamnati tun jiya juma'a a manyan biranen kasar

Yace yakamata Amurka ta sani ba ta isa ta ba wa mutanen kasare Iran wata dabara ko tunani ba.

Kwanaki biyu da suka gabata ne mutanen kasar Iran suka fara zanga-zangar adawa da gwamnatin, Hassan Rouhani, saboda tsadar rayuwa a kasar.

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng