Sojojin ruwa sun kwato wani jami'insu da diyar sa daga hannun masu garkuwar da mutane

Sojojin ruwa sun kwato wani jami'insu da diyar sa daga hannun masu garkuwar da mutane

- Dakarun hukumar sojin ruwan Najeriya sun kwato wani jami'insu da diyar sa da aka sace

- An sace sojan ruwan da 'yar sa ranar Alhamis da yamma

- Sun cafke mutum biyar da ake zargi da satar sojan

Hukumar sojin ruwan Najeriya ta ce dakarunta sun kwato wani abokin aikinsu da 'yar sa da aka sace tun ranar Alhamis da yamma.

Kwamandan sojojin, Sam Bura, ya sanar da cewar sun kubutar da jami'in nasu da 'yar sa bayan sunyi musayar wuta da wadanda suka sace su. Kazalika ya sanar da cewar sunyi nasarar damke wasu mutane biyar daga cikin wadanda suka sace sojan yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga. Ya kara da cewar sun baza jami'ansu domin kamo su.

Sojojin ruwa sun kwato wani jami'insu da diyar sa daga hannun masu garkuwar da mutane
'Yan Bindiga

Bura ya ce "Wasu 'yan bindiga sun hada baki tare da sace wani jami'in soja da 'yar sa da misalin karfe 8 na daren ranar 28 ga watan Disamba a tsakanin garin Ozuoga/Omademe a karamar hukumar Ikwerre dake jihar Ribas. Mun aike da jami'anmu bayan mun samu labari, munyi nasarar kubutar da shi da 'yar sa, kuma mun lalata maboyar masu garkuwa da mutanen."

DUBA WANNAN:

Hakazalika, Bura, ya ce 'yan bindigar sun dade suna aikin ta'addanci tsakanin garin Ubima da wasu sassan jihar Ribas. Ya ce ko a kwanakin baya saida suka yi yunkurin sace darektan kwalejin sojin ruwa dake Ubinma, amma basu yi nasara ba.

An mika wadanda aka kama hannun hukumar 'yan sanda domin zurfafa bincike tare da gurfanar da su.

Hukumar sojin ruwan ta yi kira ga jama'a da su sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa duk inda suka ga motsin ragowar 'yan bindigar da suka tsere bayan samun raunuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng