Abin da ya sa Shugaba Buhari ya nada matattu a Gwamnatin sa – Fadar Shugaban Kasa
- Shugaba Buhari ya nada matattu a cikin Gwamnatin sa
- Fadar Shugaban Kasar tace za ta gyara kuskuren na ta
- Tun kusan bara aka yi niyyar fitar da wannan nade-nade
Mun ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi magana game da ba matattu mukami da yayi a jerin sunayen ‘Yan kwamitin Ma’aikatu da dama na Gwamnatin Tarayya ya aka fitar kwanan nan.
Mai magana da bakin Shugaban Kasar Malam Garba Shehu yace tun ba yau ba aka shirya nada mukaman ba. An dai fara yin aikin ne tun a 2015 lokacin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Injiniya Babachir David Lawal.
KUKARANTA: PDP tayi kaca-kaca da Gwamnatin Shugaba Buhari kan nada matatu
Ce-ce-ku-ce daga Gwamnonin Jihohi ya sa aka mikawa Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo sunayen wadanda aka nada domin ya kara dubawa. Sai dai bayan nan ne Shugaban Kasar ya fara fama da rashin lafiya.
Shehu yace sai yanzu ne Shugaba Buhari ya nemi a kakkabe sunayen wadanda aka ba mukaman wanda shi kuma Sakataren Gwamnati na yanzu Boss Mustapha yayi abin da aka sa shi. Buhari yace za a gyara kuskuren da aka yi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng