Malamin Addini ya rataye kansa a Kaduna
- Wani Malamin addini mai shekaru 40 ya kashe kansa
- An samu gawar sa ranar Juma'a a rataye jikin fankar dakinsa
- Ana zargin ya kashe kansa ne saboda mutuwar Matar sa a 2015
Wani Malamin addini, Samuel Hamza, mai shekaru arba'in a duniya ya kashe kansa a unguwar Rimi dake cikin garin Kaduna.
Kafin mutuwar sa, Hamza ya kasance limami ne a wata majami'a dake unguwar. Ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a jikin fankar dakinsa.
Makobatansa sun samu gawar sa tana reto a jikin fankar dakinsa.
DUBA WANNAN: 'Yan Sara-Suka wadanda akafi sani da 'yan shara 27 sun fada komar 'yan sanda a jihar Kaduna
Duk da ba'a san takamaiman dalilin da ya saka Hamza ya kashe kansa ba, makobatansa sun bayyana cewar yana fama da matsananciyar damuwa tun bayan mutuwar matar sa a shekarar 2015. Saidai, sun bayyana mamakinsu ga abinda malamin ya aikata.
Makobtan marigayi Hamza sun bayyana shi a matsayin mutumin kirki dake zaune da jama'a lafiya.
Hamza ya rasa matar sa da suka haifi da daya tun a shekarar 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng