Aisha Buhari ta koma a asibitin da Yusuf ke jinya

Aisha Buhari ta koma a asibitin da Yusuf ke jinya

- Yusuf Buhari ya fara farfadowa a asibitin da yake jinya a Abuja

- Fadar shugaban kasa bata cikin matsin da zai sa ta kai Yusuf Buhari jinya kasar waje

- Yan siyasa da mayan ma'aikatan gwamnati suka fi zuwa duba Yusuf a Asibitin da yake jinya

Legit.ng ta samu rahoton cewa fadar shugaban kasa bata cikin matsin da zai sa ta kai yaron shugaban kasa Muhammadu Buhari jinya kasar waje.

Rahoton da aka samu daga majiya mai karfi ya nuna cewa, yaron shugaban kasa ya fara farfadowa a asbitin da yake jinya a Abuja.

Wani na kusa da fadar shugaban kasa ya fadawa manema labaru cewa, bayan hatsarin babur da Yusuf yayi a makon da ya gabata, Aisha Buhari ta koma da zama a asibitin da dan ta ke jinya dan kulawa da shi.

Aisha Buhari ta koma a asibitin da Yusuf ke jinya
Aisha Buhari ta koma a asibitin da Yusuf ke jinya

“Matar shugaban kasa ta koma zama asibti dan karban gaisuwar bakin dake zuwa yi musu gaisuwa, mafi akasarin masu zuwa duba Yusuf a asbiti yan siyasa ne da manyan ma’aikatan gwamnati.

KU KARANTA : Yi kira a gidan man fetur ka bakwanci gidan yari – Hukumar ‘yan Sanda ta yi gargadi

“An kara jami’an tsaro a cikin asibtin tun lokacin da aka kwantar da Yusuf ,” inji na kusa da su.

Ya kuma karyata zargin da ake yiwa matar shugaban kasa na cewa, ta yanke jiki ta fadi bayan ta samu labarin danta yayi hatsari akan babur.

Idan aka tuna a makon da ya gabata ne, yaron shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Yusuf yayi hatsari akan babur wanda ya janyo tashin hankali a fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: