Kishi ko hauka: Wata Mata ta kashe Mijin ta a gida saboda zargi
- Zargin banza ya sa wata mata ta kashe mijin ta na aure
- Wannan mata ta watsawa mai gidan na ta tafasasseh mai
- Mummunan abin ya faru ne ana shirin bikin idin Kirsimeti
Labari ya iso gare mu daga Jaridar Ogegist cewa wata Mata ta aika Mijin ta har lahira saboda zargin yana lalata a zaman auren na su. An faye samun irin wannan hadari musamman yanzu a Kasar nan.
Labarin ya iso gare mu na daga Jaridar kwanan nan inda aka bayyana cewa ana gobe bikin Kirismeti ne wata mata da hannun ta tayi sanadiyyar rasuwar Mijin ta saboda zargi da ya shiga tsakanin su a cikin auren na su.
KU KARANTA: Gwamnan Adamawa ya bayyana inda ya sa gaba a 2018
Jaridar tace wannan abu da faru ne a ranar 24 ga watan Disamba inda Mai dakin wannan Bawan Allah ta watsa masa tafasassehen man gyada. Wannan ne dai yayi sanadiyyar cikawar wannan Jami’in Hukumar na Kwastam.
Bawan Allan ya rasu ne a Ranar Asabar da ta wuce. Matar ta sa ta watsa masa mai ne mai mugun zafi yayin da yake cikin ban daki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng