‘Yar Autar Shugaban Kasa tayi magana game da hadarin Yusuf Buhari

‘Yar Autar Shugaban Kasa tayi magana game da hadarin Yusuf Buhari

- A Ranar Talata ‘Dan Shugaba Buhari yayi hadari

- Kanwar sa tayi magana game da abin a Facebook

- An ce babur din yayi kuli-kulin kubura a kan titi

Tun kafin dai jiya ku ka samu labari cewa Yusuf wanda shi ne kadai ‘Da Namiji wurin Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi hadari a kwanan nan a kan babur wajen wani shatale-tale a Unguwar Gwarimpa da ke Garin Abuja.

‘Yar Autar Shugaban Kasa tayi magana game da hadarin Yusuf Buhari
Ragowar babur din da aka yi hadari da shi. Hoto: Daily Trust

Yanzu haka mun samu labaru cewa Kanwar sa kuma ‘Yar autar Shugaban Kasar a Duniya watau Hanan Buhari ta rude da ta ji labarin hadarin ‘Dan uwan na ta Yusuf Buhari inda ta zo shafin sadarwa na Facebook ta bayyana yadda aka yi.

KU KARANTA: Hadarin babur: Ya abin ya kasance da Yusuf Buhari

‘Yar Autar Shugaban Kasa tayi magana game da hadarin Yusuf Buhari
‘Yar Autar Shugaba Buhari kwanaki da Mahaifiyar ta

Hanan Muhammadu Buhari kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust ta rubuta ‘SubhanalLah’ a shafin na ta. Hadarin dai ya sa ana cewa yanzu haka yaron Shugaban Kasar watau Yusuf Buhari bai san inda kan sa yake ba.

Hanan Buhari wanda ta ke aikin daukar hoto ta nuna hoton ragowar babur din bayan yayi kaca-kaca duk a shafin na ta na Facebook a jiya. Zahra Buhari dai a jiya ta bayyana cewa Yusuf din ya fara samun sauki tana mai cewa AlhamdulilLahi!

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng