Gwamnan Katsina ya sallami kwamishinan ilimi na jihar

Gwamnan Katsina ya sallami kwamishinan ilimi na jihar

- Gwamnan jihar Katsina ya kori kwamishinan ilimi na jihar

- Sallamar ta kunshi ne a cikin wata wasikar da gwamna Masari ya sanya hannu

- Masari ya ce yanzu da zabe ya gabato ya zama wajibi ga gwamnati ta kawo tsayayyar 'yan siyasa don cimma burin ta

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya kori kwamishinan Ilimi na jihar, Halimatu Idris.

Sanarwar wanda mai magana da yawun gwamnan, Abdu Labaran, ya sanya hannu inda ya ambata wasikar da gwamna da kansa ya sanya hannu, yayin da yake gode wa Misis Idris ga ayyukan da ta yi a matsayin kwamishinan Ilimi.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, a cikin wasikar wanda aka rubuta a ranar 21 ga watan Disamba, 2017, Masari ya ce tsohon kwamishinan ta bada gudunmawa a ci gaban gwamnatin jihar musamman a fannin harkokin Ilimi.

Gwamnan Katsina ya sallami kwamishinan ilimi na jihar
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina

Gwamnan ya ce, a karkashin jagorancinta, "An gyara makarantu da dama, yayin da aka gina wasu sababbin, an horar da malamai da kuma yanayin da suka dace don ilmantarwa da koyarwa".

KU KARANTA: Masari zai nada wani sabon kwamishina a Katsina

Masari ya ce, idan aka yi la'akari da cewa ayyukan yakin neman zabe ta shekara 2019 za ta fara gadan-gadan a farkon shekara ta gaba, "ya zama wajibi ga gwamnati ta kawo tsayayyar 'yan siyasa don cimma ci gaban da ake bukata".

Ya ce a madadin gwamnati da al’ummar jihar, gwamna Masari ya yi wa Farfesa Sa'adiya fatan alheri a ayyukanta na gaba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng