Jigo a jam'iyyar APC ya dauki nauyin aurar da mutane 100 a Sokoto
- Jigo a jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Umaru Kwabbo ya yi alkwarin daukan nauyin daurin auren ma'aurata 100 a jihar
- Bayan biyan sadaki, Kwabbo yace zai taimaka musu da tufafi, kayan kawata daki da garar abinci
- Kwabbo ya koka ga halin talauci da al'umma ke ciki wanda hakan ne ya hana samari da dama yin auren
Jigo a jami'iyyar APC kuma gogagen dan siyasa a jihar Sokoto, Alhaji Umaru Kwabbo ya dauki alkwarin daukan nauyin aurar da mutum 100 a jihar na sokoto.
Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, Kwabbo ya bayyana hakan ne a yayin da ya hallarci taron addu'a da aka gudanar a gidan sa da ke garin Sokoto.
Legit.ng ta tattaro cewa jigon ya yi alkawarin aiwatar da wannan gagarimin aikin ne domin rage adaddin matasa da samari da marasa aure a jihar. Ya lura cewa da yawan su na son yin auren amma rashin abin hannu ne ya hana su.
DUBA WANNAN: Karancin man fetur zai gushe nan bada dadewa ba - Manyan dilalan man fetur
Bayan biyan sadakin auren, Kwabbo yace zai basu kyautan garar kayan abinci, tufafi, kujeru, gado da sauran kayan kawata daki.
A wani labari mai kama da wannan, Legit.ng ta baka rahoton inda hukumar Hisba na jihar Kano itama ta bayyana shirye-shiryen da ta keyi na aurar da zaurawa 2000 a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng