Kirsimati: Yan Shi’a sun ziyarci cocina, sun wanzar da zaman lafiya
A ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, Mambobin kungiyar Musulman Shi’a sun kai ziyara wasu daga cikin cocinan dake jihar Kaduna da Jos domin taya Kiristoci bikin Kirsimati tare da wanzar da zaman lafiya a kasar.
Kungiyar yan shi’an wanda suka ziyarci cocim Evangelical Church Winning All (ECWA) Marafa Estates, sunce addinin Musulunci addinin zaman lafiya ne sannan kuma wanzar da zaman lafiya tare da makwabci yana daya daga cikin koyarwar annabi Muhammed.
Jagoran tawagar Dr Shuaibu Musa yace: “Mun zo nan domin taya yan uwanmu Kirista murnar zagayowar ranar haihuwar wanda annabinmu ya tabbatar da dawowarsa bayan bayyanar Imam Mahdi.
“Zan kare addininsu da cocinansu a ko ina suke. Muna rike da wannan alkawari shiyasa shugabanmu Sheikh Ibraheem Zakzaky ya nuna mana cewa Kiristoci ba makiyanmu bane amma yan uwanmu ne kuma makwabtanmu.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)
“Sai mun hada kaine zamu cimma hadin kai tsakanin dukka addinai tare da guje ma fitinannun shugabanni." Inji shi.
A nashi jawabin, Rev. Sule Mashan yace Allah ne ya hallici mutane sannan kuma yayi wasu Musulmai wasu Kirista. Don haka yayi kira ga addinan biyu da su fahimci junansu.
Har ila yau mabiya Shi'a sun kuma kai ziyara wani coci mai suna 'Fatima Cathedral Church' dake garin Jos.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng