Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)

Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)

Rahotanni sun kawo cewa a ranar Juma’a da ta gabata gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagoranci gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu ya aurar da ‘yan mata marayu guda hudu dake gidan marayu na jihar.

An daura auren ne a fadar mai martaba sarkin Gwandu, bayan shi da kansa Gwamna Bagudu ya tsaya a matsayin waliyin amaren wanda tuni sun kammala karatunsu harma da koyon aikin hannu.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yi kira ga masu kudi da su kasance masu tallafawa marasa galihu.

Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)
Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar

An daura uren yan matan ne kan sadaki naira dubu 40 ko wannensu.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya karfafa ma sojoji dake yaki da Boko Haram gwiwa (hotuna)

Bayan gudanar da walima a gidan Dakta Hali Bala, daga bisani uwargidan gwamnan ta yi wa amaren nasiha akan rayuwar zaman gidan miji.

Karin hotuna a kasa:

Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)
Gwamnan jihar Kebbi tare da daya daga cikin amaren

Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)
Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar

Gwamnan jihar Kebbi ya aurar da 'yan mata marayu 4 dake gidan marayun jihar (hotuna)
Amaren

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng