Yadda wahalar man fetir ta ragewa bikin Kirsimeti armashi a Najeriya
- A yau ake bikin kirsimeti a fadin duniya
- Wahalar man fetir na kara kamari a Najeriya
- Da yawan 'yan Najeriya sunana layin mai a wannan rana ta kirsimeti
A yau ne ake bikin kirsimeti a duk fadin duniya, kuma Najeriya ma ta bi sahun ragowar kasashen duniya domin murnar zagayowar wannan rana. Saidai bikin na kirsimeti a wannan karo ya samu raguwar armashi saboda wahalar man fetir da ta kunno kai tun farkon wannan wata.
Tun da duku-dukun safiyar wannan rana ta Kirsimeti dubban ababen hawa suka yi cuncurundo a kalilan din gidajen man fetur dake bude domin su samu man da zasu yi zirga-zirga a wannan rana. Da yawan gidajen Mai a biranen Najeriya a rufe suke saboda rashin fetir din da zasu sayar ga jama'a.
DUBA WANNAN: Hukumar NNPC ta shawo kan matsalar man fetur dake addabar Najeriya - Kungiyar IPMAN
Har yanzu babu alamun samun saukin layikan ababen hawa a gidajen Mai duk da ikirarin da kamfanin Mai na kasa (NNPC) ya yi a ranar Juma'a na cewar ya kara adadin man fetir da yake bayarwa a rana daga lita miliyan 35 zuwa lita 80. Wannan wahalar Mai ta tilasta mabiya addinin Kirista da dama zama a gidajen su yayin da wasu ma suka rasa ababen hawa da zasu kai su gida domin yin bikin ranar Kirsimeti da iyalin su.
Rahotannin jaridu ya bayyana cewar ana sayar da lita guda ta man fetir a kan N350 zuwa N600 al'amarin da ya jawo karin kudaden motocin haya tare da takaita zirga-zirga a wannan lokaci na bukukuwa.
Saidai kungiyar IPMAN ta sanar da cewar matsalar wahalar man ta zo karshe domin hukumar NNPC ta kara adadin tankokin mai da take bawa kungiyar dillalan man domin ganin ya wadata a lungu da sakon Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng