Sarkin Musulmi ya mika sakon murnar kirismeti ga kirisotocin Najeriya
- Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga kirisrocin a lokacin bukin Kirismeti
- Ya yi kira ga kiristocin Najeriya suyi koyi da halaye irin na Annabi Isa (AS) da suke murnar zagayowar ranar haihuwar tasa
- Ya kuma shawarce kiristocin su zama masu yi ma kasa addu'a domin samun zaman lafiya da cigaba masu daurewa
Sarkin musulmi, kuma shugaban majalisan kolin addinin musulunci a Najeriya, Alh. Muhammadu Sa'ad Abubakar ya mika sakon taya murnar bukin kirisimeti ga dimbin mabiya addinin kirista a Najeriya .
Sakon yana dauke ne cikin wata sanarwa da ta fito daga Sakatare Janar na Kungiyar majalisar koli na addinin musulunci na kasa, NSCIA, Salisu Shehu da ya aike ga jaridar Premium times a ranar Juma'a.
A sakon, Sultan Sa'ad Abubakar ya jadada cewa bukin Kirisimeti wanda akeyi domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (AS) a turance Jesus lokaci ne da ya dace al'umma su kara nuna kauna, tausayi da jin kai kamar yadda halayen Annabi Isa suke.
KU KARANTA: Musulmin kasar Indonesia sunyi alkwarin bada kariya ga Kirista ranan kirsimeti
Sultan ya kuma yi musu fatan alheri da addu'an samun dacewa a lokacin da suke shagulgulan kirisimetin. Ya kuma yi kira ga mabiya addinin na kirista da su cigaba da kira kan hadin kai, fahimtar juna, zama lafiya da cigaban kasa.
Gwamantin tarayya da bayyana ranakun Litinin, 26 ga watan Disamba da kuma Talata, 27 ga watan Disamba a matsayin rannakun hutun.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng