Musulmin kasar Indonesia sunyi alkwarin bada kariya ga Kirista ranan kirsimeti
- Musulmin sun dauki wannan matakin ne saboda barazanar kai hari da suka yawaita sakamakon yunkurin shugaban Amurka, Donald Trump na mayar da Qudus babban birnin Isra'ila
- Shugaban matasa na kungiyar musulunci mai suna Nahdlatul Ulema, Yaqat Chiolil Qoumas ya bayar da sanarwan
- Musulman kasar Indonesian sun ce a shirye suke su ba wa abokan zaman su kariya ranar Kirsimeti idan su bukace su da yin hakan
A halin yanzu da kasashen duniya ke kara inganta tsaro domin shagulgulan Kirsimeti, al'ummar musulmin kasar Indonesia sun bayyana niyyar su na taimakawa wajen bayar da tsaro a coci-cocin kasar a ranar Kirsimeti.
Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin shugaban matasa na kungiyar Nahdlatul Ulema, Yaqat Chiolil Qoumas. Kungiyar tana daga cikin kungiyoyin musulunci mafi girma a kasar.
Legit.ng ta tattaro cewa barazanar kai hare-hare sun yawaita ne tun bayan yunkurin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi na mayar da Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila duk da cewa galibin kasashen duniya sun nuna kin amincewar su da hakan.
DUBA WANNAN: Gwamnati ta bawa Ekweremadu, Bankole da Katsina-Alu wa'adin kwanaki 21 su fice daga gidajensu
Yaqat yace idan yan uwansu maza da mata kirista na bukatar tsaro domin suyi bukukuwan Kirsimeti cikin kwanciyar hankali, toh zasu taimaka.
Gabanin bukin da za'a gudanar karshen wannan makon, gwamnatin kasar ta baza jami'an tsaro da kyamaran tsaro na CCTV a wurare daban-daban a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng