Shugaban kasar Najeriya: Ya al’amarin yake?
Shin kun taba tunanin abun da shugaban kasar Najeriya ke karba a matsayin albashi? Shin kana da burin zama shugaban kasa sannan kana son sanin ainayin albashin da babban kwamandan kasar ke samu? Ci gaba da karatu domin sanin bakin zaren!
A lokacin da Muhammadu Buhari ya hau kujerar mulki- daya daga cikin shawarwari da ya yanke shine rage yawan kashe-kashen kudi a gwamnati. Hakan bai shafi albashin mataimaka da ma’aikatan gwamnati kawai ba amman harda nashi albashin.
Muhammadu Buhari ya yanke yawan albashi da shugaban Najeriya ke karba da 50%. Ya yanke albashin mataimakinsa da kashi biyu.
Menene albashin shugaban kasar Najeriya a shekara? Ya kai kimanin naira miliyan goma sha hudu. Wannan yana nufin cewa shugaba Muhammadu Buhari yana tafiya da naira miliyan daya a kowani wata. Amman kada ku manta cewa shugaban Najeriya yana samun gatanci daga gwamnati. Ya hada da kudin alawas alawas na yau da kullun, kamar kudin wahalhalu (kimanin naira miliyan 1.8) da alawus na dagewa (kimanin naira miliyan 8.8) a shekara.
Sauran alawus-alawus na yau da kullun sun hada da;
Kudin Shan man fetur;
Kudin amfani;
Kudin liyafa;
Kudin tsaro;
Kudin ma’aikatan gida;
Kudin mataimaka na musamman;
Kudin mataimaki na sirri;
Gwamnati ce take samar da wadannan alawus alawus din. Ba albashi kadai shugaban Najeriya ke karba ba daga gwamnati ba. Yana iya more kudin alawus na rangadi, alawus na kiwon lafiya, alawus na masauki, da alawus na kayan daki.
Ya kamata ku lura cewa Muhammadu Buhari ya yanke Albashinshi ne da kashi biyu a lokacin da hau kujerar mulki.
Saboda haka, albashin tsoffin shugabannin kasa ya kasance kashi biyu. Idan ka hada kudin dala daya a lokacin tsohon shugaban kasa –kana iya ganin girman albashin sosai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng