Kungiyar asiri ta sake kunno kai yayin da rayukan mutane hudu suka salwanta a jihar Legas

Kungiyar asiri ta sake kunno kai yayin da rayukan mutane hudu suka salwanta a jihar Legas

Wani iyali da ya kunshi uba, uwa da kuma dan su, sun halaka a safiyar ranar Alhamis din da ta gabata, yayin da wasu 'yan kungiyar asiri suka katse musu hanzari a yankin Ibeshi na Ikorodu dake jihar Legas.

Hakan ya faru ne bayan wata kungiyar asiri ta hallaka wani mutumi a hanyar PPL dake karamar hukumar Ojo a jihar.

Wani bako da ya kawo ziyara gidan wannan iyali domin bikin kirsimeti ya tsallake rijiya da baya, inda a halin yanzu yake karbar magani a asibiti sakamakon raunuka da 'yan kungiyar asirin suka yi sanadi.

Rahotanni daga shafin Vanguard sun bayyana cewa, kungiyar asirin ta kai hari kan wannan iyalin ne a yayin da suke bacci cikin dare.

Yankin Ikorodu na jihar Legas
Yankin Ikorodu na jihar Legas

Wannan hare-hare sun afku ne bayan kimanin mako guda da sanarwar kwamshinan 'yan sanda na jihar, Imohimi Edgal, ta cewa an samu raguwar kimanin kaso 35 na hare-hare na 'yan kungiyar asirai sanadiyar kai komo ta 'yan sanda a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Wasu ma'aurata sun shiga hannun hukuma da laifin cin zarafin mai aikin su

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda tuni ta killace gawarwakin wadanda abin ya shafa bayan da aka tsinto gawar mutumin nan guda a kan hanyar Ojo ta unguwar Okokomaiko.

Wata mazauniyar wannan yanki, Misis Adebisi Olapeju ta bayyanawa manema labarai cewa, harin ya afku da safiyar ranar Alhamis din da ta gabata, inda ta kara da cewa 'yan ta'adda sun bude wuta kan mai uwa da wabi a yayin kai harin

A yayin wallafar wannan rahoto, anyi rashin sa'ar jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, Chike Oti, inda yace ayi mishi uzuri sai zuwa lokaci na gaba.

Latsa wannan sabuwar manhajar samun labaran Legit.ng Hausa cikin sauki a wayoyinku na salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng