Gwamnatin Katsina za ta dauki ma’aikatan shirin N-Power aiki na dindindin
- Gwamnatin Katsina ta yi alkawari za ta dauki ma’aikatan N-Power aiki na dindin din a ma’aikatar gona
- Masari ya ce gwamnatinsa a shirye take domin ci gaba ta tallafawa tare da samarwa matasa aikin yi
- Gwamnan yayi kira ga matasan jihar da kada su raina sana’a ko ya take
Gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Aminu Bello Masari ta bayyana tabbacinta na daukar ma’aikatan shirin N-Power da gwamnatin tarayya ta turowa ma’aikatar gona ta jihar.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari , babban darakatan hukumar ma’aikatar gona ta jihar (KTARDA), Alhaji Ibrahim Shehu Musawa ya sanar da hakan a lokacin da ake gudanar da taron bita na sabbin ma’aikatan N-Power a babban dakin taron EEC dake cikin Katsina, babban birnin jihar.
Daraktan ya ci gaba da cewa a bisa kokarin da gwamnan jihar ke yi wajen bai wa harkar gona fifiko a gwamnatinsa ya sa jihar Katsina ta cikin jihohin dake tunkaho da albarkar nona.
Idan baku manta ba a farkon makon nan ne gwamnan jihar yayi kira ga matasa da kada su raina sana’a ko ya take domin rike ta ya fi rufin asiri da daukakar daraja a cikin al’umma.
KU KARANTA: Zaben 2019: Hotunan tsayar da shugaban kasa Buhari ya billo a Ilorin
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa a shirye take domin ci gaba ta tallafawa tare da samarwa matasa sana’o’in da za su rike kawunan su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng