Yadda rundunar soji ta sauya rayuwar mijina zuwa abun da bai taba mafarkin zama ba – Inji wata mata

Yadda rundunar soji ta sauya rayuwar mijina zuwa abun da bai taba mafarkin zama ba – Inji wata mata

Wata mata ta ba da takaitaccen tarihin yadda rayuwar mijinta ya kasance bayan mafarkinsa ya zamo gaske.

Ta bayyana yadda rayuwar ta ita kanta ya kasance lokacin da mijin nata ya shiga garari a lokacin yana matashi ccike da kuruciya.

Har ila yau ta sanar da yadda Allah ya kawo dauki ga mai gidan nata ta hanyar turo masa wani da ya kawo sauyi a cikin rayuwarsa bayan ya taimaka masa da hanyar da ya kai shi ga zama soja.

Yadda rundunar soji ta sauya rayuwar mijina zuwa abun da bai taba mafarkin zama ba – Inji wata mata
Yadda rundunar soji ta sauya rayuwar mijina zuwa abun da bai taba mafarkin zama ba – Inji wata mata

Ta fara bayani kamar haka: “Mijina ya bar gida yana matashi ya koma yawon unguwa. Yayi rayuwa cikin mawuyacin hali.

"Daga karshe ya samu aiki a shagon kanikawa inda ya samu sana’an yi. Wata rana wani babban hafsan soja ya kawo mishi gyaran mota.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun fi iya rike iyalansu – Inji wata mata dake alfahari da auren soja

"Mutumin ya ga kwazo a tattare da shi sai ya tambayeshi ko yana da burin zama soja. Sai yace eh. Sai ya shiga aikin soja. Ya sa kwazo sosai a aikin sojan, yayi karatu har zuwa matsayin digiri. Mutumin da ya taimaka mishi ya sa ya jajirce.

"Yana alfahari da kasancewarsa soja saboda aikin soja ya bashi duk wani abu da bai taba mallaka ba: daidaituwa, damar karatun boko, tsayayyen aiki. Aikin soja ya kawo masa sauyi a rayuwarsa matuka”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng