Sojoji sun fi iya rike iyalansu – Inji wata mata dake alfahari da auren soja
Kamar yadda kuka sani mutane da dama kan ci tsoron abun da zai hada su tarayya da sojoji, sakamakon wannan kallo da ake masu a matsayin mutane masu bodadden ra'ayi.
A bangaren wata mata da ba’a bayyana sunanta ba ta bayyana yadda take alfahari da kasancewarta matar soja.
A cewarta bata taba yin danasin aurenta ga soja ba saboda an horar dasu kan yadda zasu riki iyalinsu cikin so da kauna tare da kulawa na musamman.
Matar ta bayyana ra’ayinta kamar haka: “Ina alfahari da auran jami’in soja. Na fara rayuwar aurena da soja sannan bana iya kallon kaina tare da dan farin hula. An horar da jami’an sojoji kan yadda zasu kula da iyalansu, ina son haka.
“Duk abun da suka samu sun aba matansu. A koda yaushe suna so suga yayansu cikin yalwatacciyar rayuwa. Hatta da katin cire kudinsu na ATM yakan kasance tare da matarsu saboda sukan kasance a wajen da basu iya yi mata aiken kudi.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa Atiku ya sauya sheka daga APC zuwa PDP - Kungiya
“Wasu sojojin ma sukan ba mace kudi ta gina gida saboda su basa zama a koda yaushe, mace ke biyan kudin makaranta, siyan abinci.
“A koda yaushe yana so mace ta riki iyalansa da kyau. Mutane basa sanin yadda suke ga iyalansu saboda suna yi masu kallon mutane masu wuyan sha’ani amma tare da iyalansu sun kasance masu kula matuka.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng