Sanatan Zamfara yayi kaca-kaca da Gwamna Abdulaziz Yari
- Sanata Kabiru Marafa ya caccaki Gwamna Abdulaziz Yari
- Kabiru Marafa yace Gwamna Yari ba asalin ‘Dan Jihar bane
- Kusan dai ba a jituwa tsakanin Sanatan da Gwamnan Jihar
Sanata Kabiru Marafa na Yankin Jihar Zamfara ta tsakiya yayi kaca-kaca da Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari kamar yadda mu ka samu labari a wani zaman Majalisa wannan makon daga Daily Trust.
Shugaban kwamitin harkar man fetur a Majalisar Dattawa Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari da kan sa ba asalin 'Dan Jihar Zamfara bane. Hakan dai ya ba Jama’a da dama mamaki.
KU KARANTA: Majalisar Dattawa tayi kaca-kaca da Ibrahim Magu
Kamar yadda mu ka ji, Sanatan ya bayyana wannan ne wajen tantance wani Kwamishina zabe da Shugaba Buhari ya aika sunan sa zuwa Majalisar Dattawan. Idan hara an amince da shi, Kwamishinan zai yi aiki ne a Jihar Zamfara.
Sai dai Gwamnan ya nemi kar a tantance wannan Kwamishina na INEC inda shi kuma Sanatan Jihar yake ganin Ahmad Bello Mahmud ya cancanta, A nan ne Sanatan ya fadawa ‘Yan uwan sa cewa Gwamnan Jihar ba ‘dan Zamfara bane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng