Kayatattun hotunan faretin kammala bayar da horo ga sabbin sojojin kasa a Jaji
Shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ziyarci barikin sojoji ta jaji da ke garin Kaduna domin halartar faretin kammala bayar da horo ga sabbin Sojoji kasa.
An gudanar da faretin girmama wa gareshi, kuma shugaban sojin na kasa ya mika lambar yabo ga sojojin da suka nuna kwazo a yayin da ake basu horon.
A jawabin sa, shugaban dakarun sojin na kasa ya taya su murna sannan ya shawarci sabbin sojojin sun zama masu kishin kasa da gudanar da aikin su bisa yadda doka ta tsara a duk halin da suka tsinci kansu.
DUBA WANNAN: Sifeta Janar Idris ya kira kwamandojin SARS zuwa Abuja don horaswa
Sauran manyan sojoji da sauran al'umma duk sum sami hallara taron. Ga hotunnan yadda bukin ya kasance a kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng