Soyayya gamon jini: Saurayin ɗiyar Gwamna Ganduje, Fatima, ya sanya mata zoben neman aure
Diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Fatima Ganduje ta daura hotunan saurayinta, yayin da yake bayyana mata soyayyarsa, ta hanyar bata zobe kamar yadda ake yi a kasashen turai.
Fatima ta bayyana wannan hotuna ne a shafinta na kafar sadarwar zamani, Instagram, inda a cikin za’a ga saurayin nata, Idris Ajimobi, yaron gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya na sanya mata zoben soyayya.
KU KARANTA: Ashsha! Wani Dangaruwa bahaushe ya kekketa maƙogoron budurwarsa a Legas
Legit.ng ta ruwaito Fatima ta kara da wasu kalaman soyayya, inda take cewa:
“Ina cikin kwanciyar hankali matuka, Idris ka sace zuciya ta, ka cika min ita da farin ciki, duk da cewa gaba daya bamu wuce shekara daya ba muna soyayya, ka nuna min kauna, ka sanya ni dariya, sa’annan ka na mutunta ni.
“Kai ne sarkin zuciya na, kai ne garkuwa na, ka bude min ido da tsananin soyayyar da ka nuna min, ka bayyana min kauna ta yadda bana tunani, don haka a yau ni ke da riba, ina kaunar ka Idris, kuma nice matar da zaka so har iya rayuwar ka har ma a lahira. Ya masoyina.”
Idan za’a tuna a watan daya gabata ne gwamna Ajimobi ya jagoranci tawagar yan uwa da abokan arziki zuwa jihar Kano don nema ma dansa auren Fatima a hannun gwamna Ganduje.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng