Bikin Kirismeti: Gwamnati ta bayyana ranakun hutu a Najeriya
- Za a yi hutun kwanaki 3 a Najeriya ba tare da zuwa ofis ba
- Lokacin bikin Kirismetin mabiya addinin Kirista ya karaso
- Sannan kuma za ayi murnar shiga sabuwar shekara a Kasar
Labari ya iso mana cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranakun hutu a Najeriya ta bakin Ministan harkokin cikin Abdurrahman Dambazau yayin da ake shirin ayi bukukuwan Kismeti da kuma sabuwar shekarar miladiyya.
Kamar dai yadda aka saba Gwamnatin Najeriya ta ayyana Ranar Litini mai zuwa da kuma washe-garin Ranar watau 25 da kuma 26 na Watan Disamba a matsayin Ranakun hutun Kirismeti na da dama na mabiya addinin Kirista a Kasar.
KU KARANTA: Jam'iyyar adawa a Najeriya ta burma sabon rikici
Bayan nan kuma akwai wani hutun a Ranar 1 ga Watan Junairu wanda shi ma ya fado a Ranar Litinin Ministan Kasar Abudrrahman Dambazzau ya bayyana wannan ta bakin Sakataren din-din-din na Ma’aikatar sa Abdubakar Magaji.
Sanarwar dai ta zo mana a jiyan ne inda Gwamnati ta nemi a kara hada kai domin zama lafiya a Najeriya. An kuma nemi ‘Yan kasar da su cigaba da marawa Gwamnatin Shugaba Buhari baya yayin da yake kokarin gyara Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng