Dandalin Kannywood: Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale

Dandalin Kannywood: Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa yanzu haka akwai soyayya mai karfi a tsakanin fitattun jaruman nan na fina-finan Hausa watau Baballe Hayatu da kuma Sadiya Gyale.

Kishin-kishin din soyayyar ta su ma dai ya kara karfi ne bayan da wasu zafafan hotunan su suka fita a kafafen sadarwar zamani dauke da su cikin irin siga ta ma'aurata ko kuma ta masu shirin aure.

Dandalin Kannywood: Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale
Dandalin Kannywood: Ana kishin-kishin din soyayya ta shiga tsakanin Baballe Hayatu da Sadiya Gyale

KU KARANTA: Wani dan garuwa ya kashe budurwar sa a Legas

Legit.ng dai ta samu cewa shi Baballe Hayatu yana daya daga cikin manyan maza da suka dade suna harkar fim din amma kuma har yanzu bai taba yin aure ba watau ma'a dai shi har yanzu tazuru ne.

Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa Sadiya Gyale fitacciyar jaruma ce da ta taka muhimmiyar rawa a shekarun baya tun masana'antar fim din ma tana tasowa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng