Ikon Allah baya taba karewa: An yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Abuja da kewaye (hotuna)
Kamar yadda muka sani a kullun Allah na cikin nuna mana mu’ujiza da ishara akan al’amuran duniya.
A cikin daren jiya ne Allah ya saukar da ni’ima ga al’umman babban birnin tarayya Abuja da kewayenta.
Inda ruwan sama na bazata ya dunga kwarara tun daga misalin karfe uku na dare.
Wannan al’amari ya zamo abun al’ajabi ne domin kowaa ya san cewa ba’a lokacin damuna muke ciki ba, amma Ubangiji mai yadda yaso sai ya yi nufin saukar da ruwan sama a wanann lokaci.
Wadannan hotuna da kuke gani a kasa na rowan saman da akayi a kasuwar Zuba ne:
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Boko Haram sun sha kashi yayinda sojojin Najeriya suka kai masu hari, sun kuma samo makamai (hotuna)
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng