Abin da yake hana samarin Kano kasa zuwa zance a Barikin Sojoji

Abin da yake hana samarin Kano kasa zuwa zance a Barikin Sojoji

- Ko da yake iyaye a ko'ina zasu so a auri 'ya'yansu, basu da damar tallata su

- Gidan soja abin tsoro ne, kuma yaran soja ba'a samun ganinsu sosai a gari

- Akwai dokoki da ke hana farar hula shiga gidan soja

Sojin Bokavu Baracks sun koka kan kin zuwa zance wurin 'ya'yansu da samarin Kano ke yi
Sojin Bokavu Baracks sun koka kan kin zuwa zance wurin 'ya'yansu da samarin Kano ke yi

Koken iyayen 'yan mata kyawawa na cewa an qi zuwa aurarsu saboda iyayensu sojoji ne na da alamar gaskia, muddin mutum ya duba yadda lamarin tsaro ya dawo, da yadda ake tsananta bincike a wurin shiga kowacce bariki.

Kanawa kuwa, an sansu da son al-ada, da gargajiya, da kumma ganin sojoji a matsayin 'yan bariki ko lalatattu masu shan giya, wannan zai kashe wa samarin jiki.

DUBA WANNAN: Siyasar Kano ta Ganduje da Farfesa

Ga dai kwararan dalilai guda 5 da ka iya hana samarin Kano zuwa soyayya gidan soja:

1. Tsoron ubanta, tsoron bindiga. Duk uba yana sanya ido kan diyarsa, shi ko soja, har harbi ana gani yana iya wa kan diyarsa, musamman in ka ja ta yawon dare.

2. Tsaro da ke Barikoki, saboda yaki da ake fama dashi na ta';addanci, wanda hakan zai kashe wa mai zumudin soyayya jiki.

3. Tsoron ko tarbiyyar ubanta ta shafe ta. Ana yi wa soji kallo a matsayin 'yan bariki, to haka ma ana ma iyalansu kallon kamar 'yan barikin ne, duk da cewa barikin soja daban, bariki da holewa daban.

4. Yaran sojan basu fiyeyawo a gari ba, balle mai sanya ido ko farauta ya hango su. Da yawa suna rayuwarsu ne a cikin bariki, daga cefane har makaranta. Samari kuwa, sai kinzo wucewa suke ganinki.

5. Kanawa na da kabilanci. Yawancin soji da ke zaman bariki ba Hausa/Fulani bane, wasunsu ma ko Hausar basa ji, ko da kuwa Hausawan ne. Kabilu ne na arewa daban daban, da ma na kudancin Najeriya. Shi ko ba-Kane, yai son ace kabilarsa ya aura, duk da yakan so holewa da wasu kabilun a wajen Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng