Wani jirgin sama a Legas ya gamu da barayi bayan saukarsa kasa
- A tarihin duniya wannan shine na farko
- Jirgin ya sauka kenan amma bai kai ga tsaya wa ba
- Masu fashin sunzo da muggan makamai
A wani sabon lamari da ya faru a makon jiya a jihar Legas, sai ga wai anyi wa jirgin sama sata a titun jirgi na Murtala Muhammed da ke Ikeja, saukarsa ke da wuya yana tattakin tsayawa.
Jirgin na yawo ne, dan karami, wanda Vista Jet ke tafiyarwa. Ya iso ne daga kasar Turkiyya a talata da dare. Jirgin mai lamba 9H VFA.
DUBA WANNAN: An kori David Mark daga gidan gwamnati
A cewar majiyar tamu dai, ba wannan ne karo na ffarko da haka ta faru ba, inda matukin jirgin yace an bude kofar ne ta baya, tun kain jirgin ya tsaya, an kuma sace wa wasu kayansu da ke ajiye a cikin ma'adani na jirgin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng